Daga Bello Hamza

Hukumar kula da iyakokin ruwan kasar nan da na hukumar sadarwa na kasa sun kulla yarjejeniyar aiki tare da sauran masu ruwa da tsaki wajen samar da na’urar sadarwa ga ma’aikata masu aikin shimfida kebur da bututu na karkashin teku.

A sanarwar da mataimakin darakta a sashin hulda da jama’a na hukumar Mr Edward Osagie ya fitar, yace mahukuntan hukumomin sun cimma wannan yarjejeniya ne a birnin Ikko.

A jawabin shi wajen yarjejeniyar wanda ya samu halartar Darakta Janar na hukumar daidaita aikin gwamnati Mallam Dasuki Arabi, Shugaban hukumar NIMASA, Dr Bashir Yusuf Jamoh yace hukumar ta dukufa wajen samar da kyakkyawar yanayin gudanar da kasuwanci da kuma aiwatar da yarjejeniyoyin da Nijeriya tayi da kasashen duniya daban-daban.

Ya lura da cewa lokaci yayi da Nijeriya zata sanya idanu akan shimfida kebur da bututu a karkashin teku wanda rashin hakan na iya zama hadari ga zirga-zirgar jiragen ruwa kasancewar Nijeriya ta shiga sahun mai hulda da manyan kafofin sadarwa na duniya.

A cewar Shugaban hukumar Sadarwa na kasa, Farfesa Umar Garba Danbatta, wanda ya samu wakilcin Efosa Idehen yace tsarin da hukumar NIMASA ta samar na tattaunawa da masu ruwa da tsaki zai samar da gagarumar nasara akan manufar da aka sanya a gaba.

A nashi tsokacin, Mallam Dasuki Arabi ya yabawa hukumar NIMASA da na hukumar Sadarwa na kasa dangane da yin hadin gwiwa wajen dakile babbar barazana da ka iya tunkarar kasar nan a nan gaba.

Hukumar NIMASA ta kuma sanar da masu aikin shimfida kebur da bututu a teku dangane da sabbin tsare-tsaren da take da shirin aiwatarwa biyo bayan yarjejeniyoyin da tayi da hukumomi da kasashen ketare da zimmar bunkasa tattalin arzikin Nijeriya.

Wasu daga cikin wadanda suka halarci taron sun hada da jami’an ma’aikatar muhalli na tarayya da kuma wakilan kungiyar ma’aikata masu aikin shimfida kebur da bututu na teku.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *