Hukumar kula da iyakokin ruwan kasar nan wato NIMASA ta samu lambar yabo na girmamawa daga cibiyar kwararru akan harkar haraji, inda shima Shugaban hukumar ya samu lambar yabo daga cibiyar a wajen taron liyafar cin abincin daren da ya gudana a birnin Legas.

A wata sanarwar da mataimakin darakta a sashin hulda da jama’a na hukumar, Mr Edward Osagie ya rabawa manema labarai yace hukumar NIMASA ta samu lambar yabon ne a kokarin ta na kiyaye dokokin da suka shafi biyan haraji da ayyukan jin qai da hukumar ke yi a fadin kasar nan da kuma bada gudunmawar kayayyakin aiki da nufin inganta rayuwar masu kananan sana’o’in don habbaka tattalin arzikin kasa.

A ta daya bangaren kuma, Shugaban hukumar ta NIMASA ya samu lambar yabo ne a kokarin shi na tabbatar da ayyukan hukumar sun tafi daidai da na zamani.

Idan ba a manta ba, Dr Bashir Yusuf Jamoh ya samu lambobin yabo da dama da suka hada da babbar lambar yabo ta kasa wato (OFR) wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya bashi a kwanankin baya. Har ila yau, Dr Jamoh ya lashe lambar yabo a Shugabanci na Zik.

Ita da wannan lambar yabo da cibiyar kwararru akan harkar haraji ta baiwa Dr Bashir Jamoh ita ce ta baya bayan nan a kokarin shi wajen ciyar da tattalin arzikin Nijeriya gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *