Daga Ibrahim Muhammad Kano

Jam’iyyar ta ce ba ta yarda da sakamakon ba ne kasancewar tana zargin cewa an tafka magudi a wasu wuraren da aka yi zaben.

A sakamakon da INEC ta bayyana, jam’iyyar APC ta lashe mazabar dan majalisar wakilai na Tudun Wada da Doguwa, yayin da NNPP kuma ta samu nasara a karamar hukumar Fagge Sai zaben ‘yan majalisun dokokin jiha goma sha hudu inda jam’iyyar APC ta samu goma da Gezawa da Tudun Wada da Gwarzo da Makoda da Dambatta da Warawa da Gaya da Dawakin Tofa da kuma Takai da Wudil.

NNPP ta samu kujeru hudu, wadanda suka hada da Ugogo da Gabasawa da Ajingi da kuma Garko.

Jam’iyyar NNPP,.da ita ce ta lashe zaben gwamnan jihar. Kano ta nuna rashin gamsuwa da yadda zaben ya gudana.

Hon Umar Haruna Doguwa shugaban jam’iyyar a jihar Kano, ya ce “Akwai abubuwa da dama da suka faru waɗanda ba su gamsu da su ba,Ya yi zargin cewa an tayar da hankula a wurare da dama a lokacin zaben da aka kammala za su yi nazari kan abubuwa da suka faru da neman hanyar da za su bi dan dawo da hakkin ya’yanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *