Daga Ibrahim Muhammad Kano

Dan takarar Gwamnan jihar Kano a jam’iyyar NNPP.Injiniya Abba Kabir Yusuf ya jagoranci karbar wasu yan jam’iyyun adawa daban-daban da suka koma NNPP a karamar hukumar Nasarawa.
Taron karbar sabbin yan jam’iyyar da aka gudanar a mazabar kaura Goje ya sami halartar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar na jiha da karamar hukumar.

A jawabinsa Injiniya Abba Kabir Yusuf ya yi tambihin cewa a 2019 Mutane maza da mata sun zabe su,amma akayi zalunci aka kwace musu abinda suka zaba,cikin ikon Allah gashi lokacin ya shude suma masu kwacen daga wannan karon sun shude mulkinsu zai kare ba kuma abinda ya karawa al’ummar Kano.

Ya tabbatarda cewa zasu tabbatarda yin makarantu kyauta tun daga furamare har jami’a da tallafawa matasa dan dogoro da kai.
Sannan ya yi kira ga mutane su rike kuri’unsu gam a zaben 2023 su maimaita abinda sukayi a 2023 na zabar Abba Gida-gida kuma sun yiwa mata tanadi masu kyau da ya hada da haihuwa kyauta a Asibitoci da ciyarda yara kyauta da tallafi da sauran abubuwa da dama.

Injiniya Abba Kabir yace akwai wasu da suke bi suna sayen katunan zabe, sun yi a banza duk wanda aka baiwa kudi ya karba amma su tabbatar katinsu na nan daram, kuma in sun karba sunyi a banza domin sabon dokar zabe bai basu dama ayi musu irin abinda aka yi musu a baya ba.

Abba ya ce an sha su sun warke ba za su bada dama ayi musu abinda akayi musu a baya ba.”Duk wanda yazo yace zai sai kuri’arku kuyi masa dan Karen duka mune muka gaya muku in ma da sanda Ku rafka masa,kuma a damka shi a wajen jami’an tsaro,saboda mun tabbatar da wadannan mutanen basuda imani basa kaunar al’ummar jihar kano basa son talakawa mu kuma talakawane a gabammu baki daya'”

Yace in Allah ya yarda kwanannan zasu bude kundin zabe su fadawa al’ummar Kano me suka tanadar musu,domin wasu har sun shiga kanfen basu gayawa jama’ar Kano me zasuyi ba,duk abinda suke fada karyane su zasu zo su fadawa al’umma abubuwanda suka shirya na alheri da za suyi tareda tabbatar da yin shawarwari da al’,umma dan jin abinda suke so.

Shima a nasa jawabin dan takarar majalisar tarayya na qaramar hukumar Nasarawa a NNPP. Hon.Hasan Husain yace abinda suka gani a taron ya tabbatarda Nasarawa ta Dokta Rabiu Musa kwankwaso ce.Sannan yace a matsayinsa na dan takarar majalisar tarayya yana tabbatarwa al’ummar yankin zai kawo musu canji a wakilcinda ake musu za su kori tsari na wakilcin wakilin. wakili.

Hon.Hasan ya yi kira ga al’ummar karamar hukumar Nasarawa da cewa ranar zabe su fito su zabi NNPP daga dama har kasa.

Da yake jawabi jagoran Kwankwasiyya a karamar hukumar Nasarawa wanda shine ya jagoranci karbar wadanda suka shigo jam’iyyar ta NNPP a yankin.Alhaji Yusuf Ogan Boye ya yi kira ga al’ummar jihar Kano dama Najeriya gaba daya su fito su zabi NNPP a kowane mataki dan kaiwa ga nasara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *