Daga Ibrahim Muhammad Kano.

An bayyana dan takarar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar NNPP. Sanata Rufai Wani Hanga da cewa Mutum ne karimi da yake da halayya na dattako na kyakkyawar mu’amala da mutane wanda ya dace da takara da aka bashi.

Wani dan siyasa a karamar hukumar Birnin Kano mai suka Aminu Dada shine ya bayyana hakan da yake zantawa da yan jarida.
tm
Yace duk da ba jam’iyyar NNPP yake ba dan yanzu shi yana kan katangane baya cikin kowace jam’,iyya amma dai ya tabbatar Jam’iyyar NNPP tayi kyakkyawan tunani wajen baiwa Rufai Sani Hanga takarar dama ya yi Sanata a baya kuma. Komai hassadar Mutum.ya san shi ba irin mutanen nan bane da suke jiji dakai ko kuma mukami yasa ya guji mutane

Kullum zaka sameshi  da kyakkyawar sakin fuska da iya mu’amala dan haka yana yi masa fatan alkhairi akan ya samu nasara a wannan takara da yake.

Malam Aminu Dada yace da yake Rufai Sani Hanga Mutum ne mai.kyakkyawar aniya na alkhairi sai Allah ya yi sanadinda wani mai fuska biyu da aka baiwa takarar a farko ya yi rawa Allah kuma ya kawo Sanata Rufai da yardar Allah zai kai ga nasara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *