NNPP ZA TA TUNKARI YAKIN NEMAN ZABEN GWAMNAN JIHAR KANO CIKIN LUMANA DA KARE MUTUNCINTA–Sunusi Bature

Daga Ibrahim Muhammad Kano.

Sakamakon bude ayyukanda suka shafi yakin neman zabe na yan takarar Gwamna da Majalisun jahohi da hukumar zabe mai zaman kanta tayi dan takarar Gwamnan jihar Kano a jam’iyyar NNPP.Abba Kabir Yusuf ya yi taron manema labarai dan gayawa al’ummar Kano shirinsu na yakin zabe bisa bin doka da oda.
Mai magana da yawun dan takarar Gwamnan Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa Wanda ya yi magana a madadin Abba Kabir Yusuf yace 12 ga Satan oktoba ne hukumar zabe ta bude yin kamfe na yan takarkarin Gwamna da majalisu na jaha dan haka zasuyi yakin zabe cikin lumana dan gabatar da kudurorinsu ga jama’ar Kano na cigaban al’umma ba tareda cin mutunci ko takurawa kowa ba dan Kano jahar suce da baza su so ta shiga kowane irin yanayi mara dadi ba.
Ya yi kira ga dukkannin shugabanci da hukumomin jami’an tsaro su kasance masu adalci ga dukkan yan takarkaru na kowane jam’iyya ta gudanarda ayyukansu ba tareda saka son zuciya ba.Sun kuduri aniyar ba zasu  bar wani yaci zarafinsu ko ya hanasu damarda al’ummar Kano ke kokarin basu ta hangar kada kuri’a ba.
Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa yace cikin yan kwanaki kalilan Dan takarar Gwamnan Kano na NNPP.Injiniya Abba Kabir Yusuf zai gabatarda kudurorinsa na cigaba wanda zai tabbatarda aiwatar dasu in Allah ya kaishi ga kujerar mulki na jihar Kano a 2023.
Yace sunada yakinin cewa a wannan zabe mai zuwa mutane zasu samu damar yin zabe kamar yanda yakamata Kuma hukumar zabe zata basu abinda suka zaba kamar yanda doka ta tanada da Kuma sa ran jam’iyyarsu ta. NNPP zata zamu rinjaye kan sauran jam’iyyu duba da yanda mutane ke biyayya gareta.
Bature.yace shekara mai zuwa in Allah ya yarda jam’iyyar zata kasance mai nasara da gudanarda Gwamnati da zata tallafawa kowane bangare na cigaban al’ummar jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *