Daga Umar Faruk Brinin Kebbi

Gwamnan jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya ce noma na kan gaba wajen hada-hadar kudi ga Nijeriya kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba shi fifiko.

Gwamna Bagudu ya bayyana hakan a Birnin Kebbi a wajen bikin bude taron koyawa matasa sana’o’in hannu da karfafa gwiwar matasa don su iya dogaro da kansu na tsawon kwanaki biyar.

Hukumar kula da kayayyakin more rayuwa ta kimiyya da Injiniyanci ta kasa (NASENI) ce ta shirya shi, mai taken: “Hanyoyin noma na zamani ta hanyar amfani da ingantaccen aikin noma a jihar Kebbi”

Haka kuma ya ce” Shugaba Buhari ya jajirce sosai wajen kawo sauyi a harkar noma ta hanyar samar da isassun kudade na Kimiyya da Injiniyanci, yana mai cewa, “noma ilimi ne.

A cewar Gwamna Abubakar Atiku Bagudu, kimiyya na kara habaka amfanin gona a fadin Nijeriya tare da rage matsalolin da suka shafi fannin.

Shugaban kungiyar Gwamnonin APC ya ci gaba da cewa, kimiyya na inganta kayan amfanin gona da abin da ake samu kuma Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna himma wajen ganin kasa Nijeriya ta dogara da kanta wajen samar da abincin da ake nomawa a cikin kasar.

“National Agency for Science and Engineering  Infrastructure (NASANI) tana dauke da mafi kyawun kwakwalwa kuma tana taimaka mana wajen kara inganta aikin noma a jahohin kasar nan.

“Dole in godewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari, jiharmu da kasa baki daya, sauran kasashe na fama da karancin abinci, Amma Nijeriya ba haka take ba, sai dai karin farashi.” Inji shi.

Ya ce akwai damammaki ga matasa a harkar noma, yana mai cewa, “zaku iya zama hamshakan attajirai kuma ku kasance daidai da takwarorinku a kasashen  duniya.”

Ministan shari’a Abubakar Malami, SAN, ya ce horon zai kara  wa matasa kwarin guiwa da kuma taimakawa wajen cimma burin Shugaban kasa Muhammadu Buhari na karfafa matasa.

Malami ya ce hakan zai kara karfafa shirin samar da  abinci da tsaro gaba daya, tare da bunkasa ci gaban kasa.

Da yake jawabi tun da farko, Mataimakin Shugaban Hukumar NASENI, Farfesa Muhammed Sani Haruna ya ce an shirya taron horo na kwanaki biyar don fadakar da Matasa mahalartan dabarun noman zamani da Injiniyanci a cikin aiki gona.

Ya ce tilas ne Nijeriya ta kawar da tsarin noma na gargajiya, sannan ta yi amfani da fasahar zamani don kawo sauyi a harkar noma domin samar da abinci, wadata da kuma fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje.

Farfesa Muhammadu Sani Haruna ya bayyana irin gudunmuwar  da kuma rawa da Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya taka na ganin cewa shugaban kasa ya kafa wannan hukumar da kuma  shawarwarin da yake baiwa hukumar NASENI.

Ya kuma yabawa Ministan Shari’a bisa yadda ya taimaka wajen aiwatar da dokar kafa NASENI tare da fara gudanar da ayyukanta.

Farfesa Muhammad ya mika takardar amincewa daga shugaban kasa Muhammadu Buhari ga gwamnan jihar Kebbi domin kafa cibiyar koyar da sana’o’in hannu  a karamar hukumar Bagudo a Jihar a karkashin hukumar kula da harkokin kimiyya da kere-kere ta kasa (NASENI).

Bugu da kari ya sanar da kafa cibiyoyin sarrafa injuna da kayan aikin noma na shiyya shidda wanda aka zabo Kebbi a matsayin wurin da cibiyar ta shiyyar Arewa maso yamma zata kasance.

Daga cikin wadanda suka yi jawabi a wajen taron akwai  shugaban jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato, Farfesa Lawal Bilbis da kuma Dan takarar kujerar Gwamna a Jihar kebbi a karkashin Jam’iyyar APC, Alhaji Nasiru Idris da sauransu.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *