Daga Ibrahim Muhammad Kano

Babban mataimaki na musamman a ofishin matar shugaban kasa.Hajiya Dokta Aisha Buhari.Hon.Sani Zorro yace ofishin uwargidan Shugaban kasa na taimakawa ta amfani da damarda takeda ita ta samun tallafi daga hukumomi na Gwamnati da kuma kungiyoyi masu zaman Kansu wajen hada hannu ana tallafawa makarantu dan cigaban ilimi.

Hon.Sani Zaro ya bayyana hakane da yake zantawa da yan jarida a yayinda ya wakilci mai dakin shugaban kasa a taron tsofaffin daliban Makarantar sakandiren Gwale dake a jihar Kano.

Yace akwai makarantu guda hudu data dauka a jihar Kano da suke da tsohon tarihi da suka hada da Kwalejin Rumfa da Sakandiren Gwale da kuma ta Mata guda biyu Kwalejin Gwamnati ta mata ta Dala da kuma WTC Dala.

Shine tayi amfani da damarta akasa ofishi dake lura da bada taimako a irin wannan sashen sukazo sukayi ajujuwa suka sabunta yanayin makarantun.

Ya yi nuni da cewa ita sakandiren Gwale an samar mata ajujuwa na karatu guda 48 da rijiyoyin burtsatse dake amfani da hasken rana guda Biyu da kuma babban tankin tara ruwa mai yawa da kuma an samarda dakunan bahaya na dalibai 20 sannan ansa tubali na zamani a harabar makarantar.

Hon.Sani Zoro wanda tsohon shugaban kungiyar yan jaridane na kasa kuma tsohon dan majalisar tarayya daya wakilci Gagarawa,Gumel da Maigatari yace an gyara ajujuwa guda 27 wadanda aka gada banda sababbi da akayi,sannan an gyara dakunan bincike guda hudu da sanya musu kayan aiki da yan makaranta zasu rika nazari da bincike na kimiyya.

Yace wannan daliline yasa kungiyar tsaffin daliban ta gayyaci mai dakin shugaban kasa Uwargida Hajiya Dokta Aisha Buhari da ya wakilceta.

Hon.Sani Zoro yace Nijeriya kasace da idan tayi amfani da masu tunani da masu ilimi in sukayi amfani da baiwarda Allah ya yi mata na arziki da mutane daga. Masananta da yan kasuwa da karfinda take dashi musamman darajarta a nahiyar Afirka da kuma Duniya in wadannan suka hadu wuri guda sukayi zurfin tunani zasu iya fitarda Najeriya daga cikin halinda ta sami kanta na hayaniya kuma qasarnan zata iya zama qasa da take shugabancin bama Afirka ba harma ta wuce nan.

Zorro yace alkaluma sun nuna kasarnan nada masu ilimi da suke kasashen waje kamar Likitoci da masu fasaha da injiniyoyi wadanda anan kasar aka kyankyashesu sukaje,kuma kowace kasa kamar Indiya da Chana wadanda sukayi irin tashin gwauron zabi dinnan an san cewa sunyi amfani da irin wannan masu ilimi ne,damu bamu dasu anan da kuma na’urori da kayan aiki na can, da horo da koyo da akayi da gogewa suka ciyar da ita gaba.

Hon Sani Zarro yace dan haka suna yiwa Najeriya kyakkyawan fata cewa in Allah yaso ba za’ayi kasa a gwiwa ba,wajen amfani da damarda take dashi, amma yakamata kuma musamman shugabannin Arewa ya zamanto suna cikin shirin kota kwana

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *