Bayan zaman da babban kotun tayi a jiya, Ba a ci gaba da sauraron karar neman belin da ’yan uwa na Harkar Musulunci a karkashin Sheik Ibraheem El-Zakzaky suka shigar ba, saboda wasu batutuwan da suka shafi zaben da ke gaban Mai Shari’a Emeka Nwite na babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

A karar da aka shigar mai lamba: FHC/ABJ/CR/129/2004, cikin tuhume-tuhume bakwai da suka haɗa da Ta’addanci a kan Haruna Ali Abbas, Ibrahim Hussaini Musa da Adam Suleiman, tsawon shekaru, hakan ya sa ake tsare da su a gidan yarin dake Abuja.

Da aka shiga kotun, Mai shari’a Nwite ya ce har yanzu yana cikin shari’o’in zabe, duk da cewa an sanya ranar ne ta jiya talata domin sauraren karar.

Sai dai lauyan wadanda ake kara, Aliyu Musa Yawuri, ya roki kotun da ta saurari bukatar belin waɗanda yake karewa da aka shigar.

Idan dai za a iya tunawa dai an damke mabiyan malamin su uku ne a shekarar 2013 kuma an tsare su kafin a kai su gidan yarin Kuje.

Don haka alkalin ya dage sauraron karar zuwa ranar 7 ga watan Fabrairun 2023 domin sauraren karar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *