Daga  Bello Hamza

Rundunar sojin ruwan kasar nan ta hannantawa hukumar kula da iyakokin ruwan kasar nan wani jirgin ruwan dako mai suna “MT Sea Eunice wacce ta kama a ranar goma sha daya ga watan Augustan bara.

Da yake hannantawa hukumar jirgin, shugaban sashin gudanarwa na jirgin ruwan Navy Ship Delta, wato NNS DELTA, Kwamanda Samuel Musa yayi bayanin cewa an kama jirgin ne saboda yawaitar saba dokokin hukumar kula da iyakokin ruwan ta duniya, wacce hukumar NIMASA take bi sau da kafa.

Da yake jawabi a wajen bikin amsan jirgin, Shugaban hukumar ta NIMASA, Dr Bashir Yusuf Jamoh ya yabawa rundunar sojin ruwan dangane da wannan namijn kokarin, sannan ya jaddada aniyar hukumar wajen cigaba da yin hadin gwiwa da rundunar wajen samar da tsaro a kan iyakokin ruwan kasar nan.

Da yake karban jirgin a madadin hukumar NIMASA, Injiniya Joshua Oyadiran ya bada tabbacin cewa hukumar za ta gudanar bincike bisa tsarin dokokin ayyuka na hukumar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *