Daga Bello Hamza, Abuja

Shugaban hukumar kula da iyakokin ruwan kasar nan Dr Bashir Yusuf Jamoh ya taya ‘yan Nijeriya murnar shiga sabuwar shekarar 2023.

A wata sanarwar da mataimakin darakta a sashin hulda da jama’a na hukumar Mr Edward Osagie ya rabawa manema labarai yace Shugaban hukumar ya bukaci ‘yan Nijeriya da su kara jajircewa wajen cigaba da tabbatar da hadin kan kasa.

Ya kara da cewa duk da kalubalen da kasar nan ke fuskanta, akwai yiwuwar shawo kan wadannan matsalolin matukar ‘yan Nijeriya sun himmatu wajen hadin kai, da magana da murya daya.

Shugaban hukumar ya kuma bada tabbacin cigaba da samar da sauye-sauye masu ma’ana ta yanda bangaren ruwan kasar nan za tayi gogayya da takwarorin ta na duniya.

Dr Bashir Jamoh ya kuma yi addu’ar samun dauwamammen zaman lafiya, wadata, hadin kai da cigaban kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *