Daga Abdullahi Alhassan, Kaduna
A yunkurin su na ganin an samar da wada taccen abinci ga yan Najeriya, musamman ma abubuwan yau da kullum,da kullum ake sarrafawa don abinci, Manajan Kasuwanci na  Kamfanin fulawa wato Golden Penny, a Kaduna Mista lsrael Obefemi yace kanfanin su ya samar da ton 30 na Masara, Alkama,da  Dawa  don amfanin magidanta a shiryar arewa masu yamma da ma arewa masu gabas wanda muke kira Masalina,Dawavita, MasaFlour da ma  Masavita.
Mista Obefemi yana wannan jawabi ne a Kaduna yayin kaddamar da sabon samfurin garin masara da alkama irin sa na farko a Najeriya don masu yin waina da sauransu ya kara da cewar irin wannan samfurin zai kawo tsadar Biredi a ƙasar nan ganin cewa jama’a da dama sun karkata ne kan biredi ne don kalaci maimakon sarrafa garin masara ko alkama.
Mista Israel ya ce wan nan kyakkyawan tsari ne da zai magance matsalolin haukawar farashi kayan abinci kamar masarar dawa dama alkama,Kasan cewar su abubuwan amfani na kullum ne, kaga da wan nan sabon samfurin zai kawar da ƙaruwar tsadar Biredi da saurasu saboda samun mafita ne gasu masu amfani da kayayyakin.
Shi kuwa wani dan kasuwa dake Kaduna Alhaji Abdulsalam Abdulrazak, cewa ya yi kimanin shekaru 30 kenan yana hudda da kamfanin kuma  zasu cigaba da harka da kamfanin kasancewar sa suna samar da kayeyyaki cikin farashi mai rahusa tare kuma da kyautata kayeyyaki cikin da ya yi dai-dai da al’ummar mu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *