Daga Ibrahim Muhammad Kano

An bayyana sauya fasalin kudi da babban bankin Nijeriya ya yi da cewa yazo da sauki ba’a fuskanci wani kalubale ko tazgaro sosai ba a harkar kasuwancin hada-hadar wayar hannu.

Alhaji Ashiru Yusuf Yakasai Jami’in hulda da jama’a na kasuwar waya na titin a Bairut kuma jami’in hulda da jama’a na hadaddiyar kungiyar saida waya ta kasa reshen Kano(AMPAT) ne ya shaida hakan ga yan jarida.

Ya yi nuni da cewa dama Gwamnati ta yi kiraye-kiraye a dawo harkar hada-hadar kudi ta yanar gizo, kuma su masu sana’ar wayoyin da kwamfitoci suma suna cikin harkar POS.

Ya ce a harkar cinikayya kowace kasuwa ta wayoyi dama tuni su sunyi nisa da mu’amalar saye da sayarwa ta tura kudi ta yanar gizo da Pos sunada kwarewa sosai akai.Dan haka ma suka bada goyon baya 100 bisa 100.

Ashiru Yusuf ya yi nuni da cewa babu wata Matsala sosai da suka fuskanta tsakaninsu da abokan hulda,dan tuni sun isar da sako ga abokan cinikayyarsu musamman na kauyuka akan yanda zasuyi hulda da sauyin zamani.

Ya yi nuni da cewa duk da an sami dan tasgaro a tsarin fasalin kudin sakamakon in akayi duba da bankuna da suke jihar Kano a cikin kananan hukumomi 44 da ake dasu guda 20 ne kawai ke da bankuna.Akwai mutane dake kauyuka da kafin su zo inda banki ko pos yake su cira sai sun kashe kudi mai yawa, shine kulen,da ace Gwamnati ta bude abin yakai ko’ina an sami wayar da kai a Gwamnatance da abin bai kai ga tsamari yanda aka samu ba, dan har yanzu in aka je wasu wurare saboda rashin hada-hadar kudade a hannun mutane sun zama kamar ba kowa.

Ya ce yanzu a cikin shaguna na kasuwanninsu na waya, kusan kowane shago akwai Pos wanda a baya,l bai fi a sami kalilan da suke da na’urar ba,wannan cigaba ne sannan matasa da dama suna sana’ar pos.

Ya yi nuni da cewa a jihar Kano a kowace irin harka in aka kawo in aka sami mako biyu to zai shiga jikin mutane,yanzu an saba da yanayin kuma yama kawo habakar tattalin arziki ma, dama shine manufar Gwamnati kuma in akayi la’akari da darajar Naira ya farfado a Duniya, in aka kwatanta ta da Dala.

Ashiru Yusuf ya ce tangarda da ake samu na tura kudi ba wani abune ya jawo ba,sai yawa da aka yiwa bankuna, saboda da mutane da dama suna harkar tura kudi da karamar waya,yanzu kuma anayi da tiransifa na manhajar babbar waya, adadin wanda suke a baya yanzu ya nunka shi yasa ake samun Matsala,amma yanzu bankuna da kamfanonin waya zasu da da habaka karfin yanda za’a rika hada-hadar ba tareda tsaiko ba abubuwa su dawo cikin sauki.

Alhaji Ashiru Yusuf Yakasai ya yi kira ga al’umma musamman matasa na Arewa akan yakamata su rika irin wadannan tanade-tanade ta bincike dan gano abubuwa na tafiyar zamani tun kafin ma ya riske su domin shi tun shekaru Biyu da suka gabata ma ya shiryawa karbar wannan sauyi ta amfani da pos da tiransifa ta wayar hannu da kuma yin asusun kamfani da wannan yanayi yazo sai ya dora akai.Da matasa da yan kasuwa na Arewa sun rungumi wannan tun a baya da ba za’a sami irin matsaloli da aka samu da yawa ba, tun da a Kudancin kasarnan mai shago da bai wuce jarin N20,000 ba yanada pos Amma anan mai jarin N2,000,000 amma bai shiryawa pos ba.Dan haka matasa su zama masu tunani da wuri ta yanda zasu rungumi tafiyar zamani a koda yaushe. ya zo musu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *