Daga Umar Faruk Brinin Kebbi

A kokarinta na dakile matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi musamman a tsakanin yara mata kungiyar matan gwamnonin Arewa (NGWF) sun Kaddamar da wata cibiya ta ba da horo da kuma shakatawa a Birnin Kebbi.

Wakilinmu ya ruwaito cewa cibiyar ta mai suna( KAWARA Sports and Recreation Center) an yi ta ne domin horas da yara masu mu’amala da miyagun kwayoyi da kuma koya musu sana’o’in zamani don dogaro da kansu da wasanni kamar kwallon kafa, wasan kwallon raga, kwallon hannu da kwallon kwando da dai sauransu.

Da yake kaddamar da cibiyar a Birnin Kebbi, Babban Birnin jihar, Gwamnan jihar, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya yaba da hangen nesa na kungiyar NGWF tare da tallafa wa mazajensu don gina ingantacciyar Nijeriya.

Ya kuma kara da cewa: “Dakta Zainab Shinkafi Bagudu ta yi fice a irin ayyukan da ta yi a jihar Kebbi da kuzari da muke ganin sun bayyana hakan, a nata jawabin ta bayyana matar tsohon Gwamna, Zainab Sa’idu Nasamu Dakingari a matsayar wadda ta fara assasa ginin wannan cibiyar da ake kaddamar wa. “Hakika gwamnatin da ta shude ce ta gina wannan, amma gwamnati ci gaba ce, ku yi naku kadan, wani ya kara da kimarsa, muna fatan na gaba zai yi kyau.

“Ina kuma gode wa matata bisa irin gudunmuwar da ta baiwa kwamitin yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi na Jiha da kuma yadda ta hada baki da sauran su, musamman AIG Umar Ambursa mai ritayi, sarakunanmu, shugabannin matasa, kungiyoyin matasa, kungiyoyi masu zaman kansu da jami’an tsaro, wadanda suka ba da goyon bayasu.

Hka Kuma Gwamna Bagudu ya lura cewa ƙalubalantar matsalar shan miyagun ƙwayoyi da kuma fatauci ba ƙalubale ba ne na cikin gida ko na ƙasa amma ƙalubale ne na ƙasa da ƙasa da ke buƙatar haɗin kai da goyon bayan juna don tinkarar barazanar yadda ya kamata, inji shi”.

A nasa jawabin babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a na kasa Alhaji Abubakar Malami SAN ya yabawa Gwamna Bagudu bisa yadda ya samar da tsarin dokoki, kwamitoci da rundunonin da suka shafi yaki da matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi a jihar.

Ya ci gaba da cewa” Kokarin gwamnan ya samu karbuwa daga uwargidansa, Dakta Zainab Bagudu, kuma hakan ta shaida kuma a cikin gida ta tabbatar da hakan ta hanyar gayyata da ba kasafai ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai yaki da miyagun kwayoyi da laifuffuka da ke Geneva ya yi mata don karamata da kuma hadin gwiwa don yaki da shan miyagun ƙwayoyi a Jihar kebbi.

Ya kara da cewa” A yau mun zo ne domin karfafa wannan fada, mu karfafa kan abin da ta ke yi, mu kara ginshikin tallafi ga abin da Gwamnan Kebbi ya ke yi dangane da yaki da ta’addanci a jihar.

“Shirin na yau ya shafi yaki da jahilcin shaye-shayen miyagun kwayoyi a jihar domin rage shan miyagun ƙwayoyi wanda aka kiyasta kusan kashi 11 zuwa 15 cikin 100 a jihar,” inji shi.

Shugabar kungiyar ta NGWF Hajiya Hadiza Isma-el-Rufa’i ta bayyana taron da suka yi a Kebbi a matsayin wanda ya yi matukar nasara da kuma amfani, inda ta kara da cewa ya basu damar ziyartar ayyuka daban-daban da Dakta Zanaib Shinkafi-Bagudu ta gudanar.

Ta yabawa gwamnan jihar Kebbi bisa amincewa da dokar kare hakkin yara da kuma dokar cin zarafin mata, ganin cewa bai yi sauki ba idan aka yi la’akari da irin yanayin da muke ciki.

Haka zalika, shugabar Kungiyar Matan Gwamnonin arewa, ta ce hakan ya yi nuni da gamsuwa da cewa sanya hannu kan kudirin a yanzu zai bayar da damar gurfanar da wadanda suka aikata laifin cin zarafin mata da kananan yara, inji ta.

Bugu da kari tana kira ga jama’a da su guji nuna kyama ga wadanda aka zalunta, uwargidan gwamnan kaduna ta shawarce su da su daina bayar da labarin cin zarafi, maimakon haka su kai rahoto ga hukumomin da abin ya shafa tare da bin diddigin abin da ya dace.

A nata bangaren, mai masaukin baki kuma mai shirya taron, Dakta Zainab Shinkafi-Bagudu, ta ce kungiyar ta NGWF wuri ne da matan gwamnonin ke hada hannu da juna don tallafa wa mata, yara kanana , ta kara da cewa sun gudanar da yekuwa da fadakarwa da dama a kan shirye-shirye kamar tsaftar jinin haila. , shaye shayen miyagun kwayoyi da kuma karfafa mata da matasa.

Ta kuma bada tabbacin cewa cibiyar wasanni da nishadi ta KAWARA na daya daga cikin shirye-shiryen da ake tafkawa wanda ko shakka babu zai rage illar shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin al’umma.

Uwargidan gwamnan ta yabawa maigidanta bisa abin da ta bayyana a matsayin mara misaltuwa goyon bayansa na ganin wannan cibiya da sauran shirye-shirye ta tabbata, inda ta bada tabbacin cewa matasan Kebbi sun kasance masu hazaka, hazikan mutane da kirkire-kirkire.

Daga nan Uwargidan gwamnan ta ce kaddamarwar ya zo daidai da ranar matasa ta duniya ta 2022 mai taken: “Hadin kai, Samar da Duniya ga Duk Zamani”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *