Daga Bello Hamza, Abuja

A ranar Juma’ar nan ce, goma ga watan Maris na shekarar dubu biyu da ashirin da uku, Shugaban hukumar kula da iyakokin ruwan kasar nan wato NIMASA, Dr Bashir Yusuf Jamoh yake cika shekaru uku akan madafun ikon hukumar.

Wannan na kunshe ne a sanarwar da mataimakin darakta a sashin hulda da jama’a na hukumar, Mr Edward Osagie ya rabawa manema labarai a birnin Ikko.

Akan haka ne sanarwar ta bukaci jama’a da su ziyarci shafukan sada zumunta na hukumar a facebook, Instagram, twitter da kuma You Tube a @nimasaofficial don ganin irin nasarorin da Dr Bashir Jamoh ya samu a wadannan shekarun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *