Daga Bello Hamza

Shugabankasa Muhammadu Buhari ya amince da baiwa Shugaban hukumar kula da iyakokin ruwan kasar nan Dr Bashir Jamoh lambar girmamawa na kasa wato OFR.

Hakan na kunshe ne a wasikar da Ministan ayyuka na musamman Sanata George Akume ya aikewa Dr Jamoh inda wasikar ta bayyana cewa za ayi bikin kaddamarwar ne a ranar litinin, goma ga watan Oktoban wannan shekarar a cibiyar kasa da kasa dake babban birnin tarayya, Abuja.

Kafin kasancewar shi Shugaban hukumar NIMASA, Dr Bashir Jamoh yayi aiki a hukumar na fiye da shekaru talatin.

Tun bayan nada shi a wannan matsayi kuwa, Dr Jamoh ya kawo sauye-sauye da dama a hukumar, wadanda suka hada da aiwatar da samar da tsaro da kariya a kan iyakokin ruwan kasar wanda hakan ya taka gagarumar gudunmawa wajen dakile ayyukan mabarnata a tafkin guinea inda daga bisani hukumar kula da iyakokin ruwa na duniya wato IMB ta cire sunan Nijeriya daga jerin kasashen da ke fama da mabarnata iyakokin ruwa.

Har ila yau Shugaban hukumar ya tabbatar da samun hadin gwiwa tare da masu ruwa da tsaki a ciki da wajen Nijeriya wajen ciyar da fannin iyakokin ruwa gaba ta hanyar samar da bayanan sirri daga jami’an tsaro.

A tsokacin da Dr Bashir Jamoh yayi a kafofin sadarwan shi na zamani kuwa, ya bayyana farin cikin shi ne, inda yayi nuni da cewa a lokacin da ya fara aiki a hukumar sama da shekaru talatin da suka gabata, bai taba tunanin Allah zai kawo shi wannan matsayi na Shugaban hukumar ta NIMASA ba, ballantana har yayi tunanin samun lambar girmamawa ta kasa.

Dr Bashir Jamoh ya mika godiyar shi ga Shugaba Muhammadu Buhari da kuma kwamitin da suka zakulo shi, sannan ya kuma bayyana godiyar shi ga dukkan wadanda suke mara mashi baya a matsayin shi na Shugaban hukumar NIMASA musamman masu ruwa da tsaki a fannin kula da iyakokin ruwan kasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *