Daga Ibrahim Muhammad Kano

Kwanturola Janar na hukumar hana fasa kwauri ta a kasa.Kanar mai ritata Hamid Ali ya bayyana gamsuwarsa gameda yanda kwalejin horas da jami’an hukumar dake jihar Kano ke gudanar da ayyukan ta.

Ya bayyana hakanne a yayin da yakai ziyara kwalejin a ranar Alhamis ya ce dama makasudin zuwansa shine ya ga masu daukar horon da suka dauke su aiki wanda akwai wasu wadanda zasu gama kwananan suka zo suyi magana dasu kafin a yaye su su koyi darasi daga garesu na abubuwa da yakamata suyi bayan ya ye su.

Hamid Ali ya yin kira ga wadanda ake baiwa horon su koyi ladabi da biyyayya da kwazo don samun cigaba dan tsarin su yanzu babu yin abinda bai kamata ba,kuma duk wanda aka samu da abinda bai dace ba za’ayi masa horo mai tsanani sun gargade su akan hakan kuma suna kyautata musu zato akan zasu zama nagari.

A jawabinsa na maraba kwanturola na kwalejin horon RA.Adahunse ya ce zuwansa kano ya kai ziyarce-ziyarce na kulla dangantaka da hukumomin horo na sojojin kasa dana sama dana ruwa da sauran masu kayan sarki na jihar Kano dan gina dangantaka ya kuma ziiyarci kwamandan kwastam na shiyyar Kano da Jigawa dana jihar Kaduna.

Ya ce yanzu haka akwai masu daukar horo a fannoni daban-daban guda 1330 da wasu za su sami horo na watanni shida wasu watanni Uku yanzu haka ma wasu daga ciki na rubuta jarabawar karshe da za’a ya ye su cikin watan Yuni.

Ya ce cikin ayyukanda aka kammala a harabar kwalejin sun hada da gyaran dakunan kwana dana shan magani da wajen cin abinci da rukunin ajujuwa da gyara mazaunin kwamandan kwalejin da mataimakinsa da yin rijiyar burtsatse mai amfani da rana da aka masa tanki da sauran ayyuka da dama.

Yanzu haka ana gudanar da ayyuka daban-daban na sanya fitilu masu aiki da hasken rana da gyara dakin ganawa da jama’a da sauran muhimman ayyuka.

Daga kalubalen da suke fuskanta shine na bukatar karin dakunan jami’ai da karin ban dakunan da kayayyakin aiki na zamani da kayan sadarwa na zamani da sauran su.

Kwanturola na kwalejin horon RA..Adahunse ya yaba da irin kwarin gwiwar da babban kwanturola na kasa ke dashi a kansa sannan yace kwalejin na da kwazo da da’a da jajircewa wajen bada horo ga jami’an hukumar hana fasa gwaurin.

P

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *