Tinubu Ya Gana Da Tawagar Kamfanin Man Fetur Na Shell

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya karbi bakuncin tawaga daga kamfanin raya man fetur na Shell a babban dakin taro na Aso Rock da ke Abuja.

Tawagar Shell a ziyarar ban girma karkashin jagorancin Daraktar kamfanin, Misis Zoe Yunovic tare da Peter Costello, Osagie Okunbo, da Mar De Jong.

Babban jami’in rukunin kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPC), Mele Kyari; da kuma shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila su ma sun halarci taron.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan makamashi, Olu Verheijen; mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin kudaden shiga, Zacchaeus Adedeji; da kuma mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin sadarwa, ayyuka na musamman da dabaru, Dele Alake.

Taron na ranar Litinin ya biyo bayan komawar Tinubu Abuja a ranar Lahadi bayan da ya gudanar da bukukuwan Sallah a Legas a makon jiya.

Majiyarmu ta tabbatar da cewa an tattauna wasu muhimman batutuwa wadanda zasu rage radadin talaucin da a’lumma suke ciki a Nigeria, musamman hauhawan farashin kayan masarufi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *