‘Yan Nijeriya sun kara shiga matsanancin halin a wannan makon yayin da farashin man fetur da kayayyakin masarufi suka yi tashin gwauron zabi.

Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana cewa, hauhawan farashin kayan abinci a watan Yunin 2023, ya kai kashi 22.79 a cikin dari idan aka kwatanta da na watan Mayun wannan shekarar, da ya karu da kashi 22.41 a cikin dari. Hakan na kunshe a cikin rahoton farashin kayan abinci (CPI) na wata-wata da NBS ta fitar a makon nan.

A cewar rahoton NBS, karin farashin ya kai kashi 0.38 a cikin dari, inda rahoton ya yi karin hasken cewa idan aka duba mizanin shekara-shekara, za a ga cewa farashin ya karu ne da kashi 4.19 a cikin dari, idan aka kwatanta da wanda aka samu a watan Yunin 2022 da bai wuce kashi 18.60 a cikin dari.

NBS ta ce, an samu karuwar farashin ne a kan kayayyaki kamar su, man girki, burodi, hatsi, dankali, doya, kifi, nama, kwai, kayan lambu da sauransu.

Sauran harkokin da aka samu karin farashin su ne, sufuri, iskar gas, kayan gyaran ababen hawa, kiwon lafiya da bakin mai.

Sai dai ‘Yan Nijeriya ba su gama jimamin tsadar farashin kayan masarufin ba, kwatsam sai ga sanarwar karin farashin litar man fetur daga Naira 539 zuwa naira 617 a Babban Birnin Tarayya Abuja.

Ana kyautata zaton karin farashin man ba zai rasa nasaba da batun da ‘yan kasuwar man suka yi cewa farashin na iya kaiwa Naira 700 kan kowace lita ba a kwanan baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *