Daga Ibrahim Muhammad Kano
Tsofaffin xalibai na kwalejin Ilimi ta Kano da akafi sani da Kwalejin ilimi ta Sa’adatu Rimi yan aji na 1992 sunyi taron ciki Shekaru 30 da kammala makarantar.
Taron Wanda akayi a ranar Lahadi a xakin taro dake harabar kwalejin ya sami halartar xinbin tsofaffin xaliban da wasuv daga cikin malamai da suka koyar dasu.Da yake bayani akan maqasudin taron shugaban riqo na qungiyar.Mai sharia  Kamilu Mai Sikeli yace qungiyar ta samo asaline daga gama makarantar saboda basa haxuwa da juna sai in wani abu ya taso ko a xaurin sure ko gudan rasuwa sai suka ga da buqatar lallai suzo su haxa kawunansu ko ba komai a haxu a gaisa ayi zumunci wannan shi yasa suka fara irin wannan taro tun shekaru Bakwai daya wuce.
Yace babban burinsu shine na haxin kai da zumunci da kuma taimakawa masu qaramin qarfi da iyalan waxanda suka  rigasu gidan gaskiya na qungiyar tsoffin xaliban..
Mai Sharia Kamilu Mai sikeli yace hatta malamai na kwalejin sun yaba da taron saboda suma ana qulla musu zumunci tsakaninsu da waxanda sukayi aiki tare..
Kamilu yayi kira ga shugabanni na kowane mataki a qasarnan su baiwa ilimi muhimmanci fiye da komai domin duk al’ummarda babu ilimi a cikinta karyayyiya ce babu ita.Sunaso a baiwa ilimi fifiko fiyeda komai a rayuwa.
Shugaban tsofaffin xaliban yan aji na 92 na kwalejin ilimin na Kano yace yana tuna yanda sukasa Kansu a makaranta ba tareda tilastawar iyayensu ba suka bar gidajensu ba dan basuda shiba suka zo suka kama xakunan haya sukayi rayuwa ta karatu za suyi girki tare su kwana a xaki xaya su tashi wannan Abu inya tuna yana bashi sha’awa da jin daxi.
A yayin taron dai an miqa shaidar karramawa ga wasu daga cikin malaman kwalejin da xaliban bisa irin gudummuwa da suke baiwa cigaban ilimi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *