Daga Ibrahim Muhammad Kano

Mai dakin mataimakin Gwamnan jihar Kano kuma dan takarar Gwamna Kano a zabe mai zuwa karkashin jam’iyyar APC.Hajiya Hafsat Nasiru Gawuna tayi kira ga al’ummar jihar Kano akan su baiwa takarar Dokta Nasiru Yusuf Gawuna goyon baya.

Tace kowa yasan irin rawarda mai gidan nata ya taka a mukamai da dama daya rike wajen cigaban jihar Kano.

Hajiya Hafsat Nasiru wacce ta bayyana hakan a wani taro da al’ummar karamar hukumar Dala ta shirya na nuna goyon baya ga takakar mijin nata karkashin kungiyar DASONG da Yusuf Auwal Alawiy Shatsari ya jagoranta.

Ta yi kira ga musamman iyaye mata da ya’yansi su tsaya su jajirce lokacin zabe na Gwamna su tabbatar jam’iyyar APC da Dokta Nasiru Yusuf Gawuna ke takarar a karkashinta ta sami nasara.

Hafsat Nasiru Yusuf Gawuna ta godewa al’ummar Dala musamman kungiyar DASONG bisa irin kauna da zumunci da aka nuna mata wajen goyon baya da kokarin tabbatarda nasara Dokta Nasiru Yusuf Gawuna.
Pic.Hajiya Hafsat Nasiru Gawuna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *