Daga Ibrahim Muhammad Kano

An yi kira ga al’umma kan su komawa  Allah a dukkan al’amuransu, dan shine yake kaddara duk abinda zai faru ya faru.Alhaji Garba Ahmad Wamban Tudun  ya bayyana hakan da yake zantawa da yan jarida.

Yace duk abinda Allah ya yi sai a karba,domin shi Allah  baya yin  zalunci shi, mai adalcine,amma in kace karfin kane zai baka bazaka samu ba.

Alhaji Garba Ahmad  yace dan haka  yake shawartar jama’a, suyi abinda yakamata suyi,su sa Allah a gaba sai a sami mafita daga abubuwa dake faruwa marasa dadin ji a kasarnan.

Ya kuma nuna farin cikinsa bisa yanda jama’a na yankinda  aka haifeshi ya kuma taso a cikinsu, suka ga cewa ya cancanta aka naxashi Wambai, wannan ya nuna yana zaman lafiya da mutunci da jama’a, kuma yana alfahari da sarautar da akayi masa,  zai kuma  kara masa kaimi na yin duk wani abu da yake na taimakawa kungiyoyi na jama’a da sauran bukatunsu  a yankin da jihar Kano.

Alhaji Garba ya  kuma nuna mutukar godiya ga Dagacin Tudun Wada. Alhaji Ibrahim Aliyu bisa bashi mukamin sarautar da yin fatan Allah yasa suga amfaninsa a wajen jama’a.

Shima daya daga aminan Wamban Tudun Wada.Alhaji Nu’uman Barau Danbatta Ajiyan Kazaure yace wannan ya nuna irin kyakkyawan  halin Alhaji Garba Ahmad da yanda yake taimakawa bukatun al’umma.

Ajiyan Kazauren ya yi kira ga jama’a na unguwanni suyi koyi da al’ummar Tudun Wada wajen hada kai da suke da taimakon juna da karamci da zumunci a tsakaninsu.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *