Daga Mansur Aliyu Samaru

Dandalin Siyasa na Harkar Musulunci a Najeriya karkashin Jagorancin Sheikh Ibraheem Zakzaky ya gudanar da taruka na tsawon kwanaki 3 a cikin gida da na kaddamarwar.

(29 – 31 ga Oktoba, 2022).

Kungiyar ta kaddamar da daruruwan mambobinta wadanda za su dauki nauyin gudanar da ayyukan Forum din a shiyyar Arewa maso Gabashin kasar nan.

An gudanar da tarukan ne a jihohin Gombe da Bauchi. Wakilai daga jihohin Yobe da Borno da Adamawa da kuma Taraba na daga cikin wadanda suka samu jawabai masu zurfi a kan tsari da manufofi da ka’idojin da aka shimfida na dandalin. Wadanda suka halarci taron sun hada da Convener na kasa kodineta da sauran masu ruwa da tsaki na dandalin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *