Daga Ibrahim Muhammad, Kano
An rantsar da sabbin shugabanin  kungiyar masu saida waya da kayayyakinta da ake kira “Association Mobile Phones and Allied Products Traders”(AMPAT) na kasa reshen jihar Kano.

Taron Wanda aka gudanar ranar Asabar ya sami halartar shugabannin kungiyar na matakin kasa dana shiyyoyi da sauran masu ruwa da tsaki a harkar saye  da sayarwar wayoyin tafi da gidanka.

Da yake jawabi bayan ratsar dashi shugaban kungiyar na AMPAT na jihar Kano Injiniya Abubakar Usman Ahmad yace  a shirye suke su hada kai da dukkan yan kasuwar waya wajen yin aiki tare da fuskantar kalubalenda suke damun harkar waya da suka hada da rashin tsaro ta  yanda za’ayi kwacen waya a kawo a sayar suna so da hadn kan hukumomin tsaro za suyi maganin abin.

Yace za suyi kokarin matasa su sami jari dan dogaro dakai sannan sunada kudirin samarda wajen gyara wayoyi kari a kano saboda yanzu haka  guda Biyu me  ake dasu a jihar daya na kasuwar “Farm centre” sai na kasuwar Titin Bairut in Allah ya yarda  a wata ukun farko zasu kara yawansu yanda wanda ke Doguwa zai iya kaiwa a gyara masa waya ba tare da ya shigo Birnin Kano ba.

Shima da yake ganawa da yan jarida a yayin taron jami’in hulda da jama’a na Biyu a kungiyar ta AMPAT.Alhaji Ashiru Yusuf Yakasai yace an rantsar dasu  zasu fara aiki gadan-gadan su dora kamar yanda suka saba saboda dama sunada gogewa na kusan shekara daya a matsayinsa na jami’in hulda da jama’a na kasuwar waya na Titin Bairut.

Yace kamar yanda suketa aikace aikace a baya zasu dora da fito da sabbin hanyoyi dama sunata kiraye-kiraye ga Gwamnati saboda sunada karfi ta hanyar yan chana kuma babban matsalarda ake fuskanta na sace sacen waya da ikon Allah karkashin AMPAT akwai tsari da bibiyar dan gano wayarda aka sata zata dawo hannunsu su rikayi cikin away 24 zasu iya gano waya da aka sata kuma yana cikin kwamitin gudanarda irin wannan ayyukan.

Alhaji Ashiru Yusuf yace gaskiya sunyi farin ciki da kara da jama’a musamman shugabanni da wakilin mai girma Gwamnan Kano da wakilin mai martaba sarki da shugaban karamar hukumar Brnin Kano da sauran mutane da wakilan kamfanoni da bankuna kuka yi musu suna godiya bisa wannan  karramawa da sukayi musu na halartar taron.
Kunshin sabbin shugabannin da aka rantsar  mutun 21 sun kama aiki bayan rantsar dasu A yayin taron kungiyar ta AMPAT ta karrama wasu zababbun mutane da suka hada da Gwamnan jihar Kano.Dokra Abdullahi Umar Ganduje da kwamishinan ma’aikatar kasuwanci Batista Ibrahim Muktar da DPO na yansanda na ofishin  Nasarawa Daniel da sauran mutane daban-daban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *