Daga Idris Umar,Zariya

A jiya ne mai martaba sarkin Zazzau Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli ya cika shekaru 2 akan karagar mulkin masarautar Zauzau.

Wakilinmu na daya daga cikin wakilan kafafen watsa labarai da suka halacci fadar don shaida wannan rana.

Daga cikin abubuwan da aka gabatar a wannan rana sun hada da yin addu’a ta musamman ga sarkin da masarautar ta Zazzau baki daya karkashin jagorancin limamin Zazzau Shiek Dalhatu Dahiru.

Bayan haka angudanar da nuna majigi na tarihi.

A farko da karshen zaman da aka gabatar mai martaba sarkin na Zazzau Ambasada Nuhu Bamalli yayi jawabin godiya ga dukan jama’ar kasar Zazzau bisa bashi goyan baya da sukeyi na samar da zaman lafiya bisa haka yayi fatan Allah ya saka masu da dubul alheri ga dukkan jama’ar masarautar da al’umar Nigeriya baki daya.

Daga cikin manyan mutane da sukayi wa sarkin na Zazzau fatan Alheri akwai Dan Iyan Zazzau Alhaji Abubakar Nuhu Bayaro da sarkin yarbawan Zazzau Barisa Ishak Bayaro akwai Cif Eze Ibo da dai sauran manyan mutane na cikin garin Zazzau da wajenta baki daya.

Jama’ar kasar ta Zazzau sun nuna goyan baya wajan halattar fadar don gudanar da addu’o’i

Ayi lafiya an tashi lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *