Daga Abubakar Tahir

Da yake lamarin Ambaliya ya kazanta a garin na Ganuwar Kuka inda cikin mintuna sha biyar ruwa ya kusa gamawa da garin.

Haka tasa muka fara magana da abokan aiki dake gidajen radio da jaridu kamar Bbchausa, Daily Trust, Humanangle, Liberty, JallaFm, Raypower domin dauko abinda yake faruwa kai tsaye.

Bayan isata garin na gabatar da ID Card dina na aiki inda wasu matasa da nakega sun waye suka biyo ni domin yin hirasa dasu.

Bayan na xora musu Camera na nadi abun da suke da bukata sai na dan gusa kan domin cigaba da dauka.

Katsam sai naji an bugeni da karfi a kaina inda wayoyin dake hannuna kira Infinix da Itel suka zuge cikin ruwa.

Dagowar da zan yi ashe naga wanne dalili sai naji an ciga da dukana ta koina ana buga cikin wani rafi da suke kira ruwan Makasa.

A haka suka yi ta dilmiya kaina suna dukana wasu suna cewa ku dake shi Nikwa inata kokarin nusar dasu ID card dina ina ce musu aiki nake.

A haka de wasu mutane suka yi maza suka hanasu wanda daba Dan an kawomin daukin ba da tuni sun kasha ni tunda a take wasu sun zare wuqaqe.

Haka aka kaini gidan maigari ya bani ruwa na yi wanka ya bani sabin kaya na saka Inda ya bukaci na dawo na cigaba da aiki nace masa a a.

Ya bada babura aka kawoni Hadejia inda a take na tafi babban asibitin Hadejia domin jinya.

Ya zuwa yanzu na dawo gida ina cigaba da karban magani.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *