Daga Ibrahim Muhammad Kano

Dandazon dubu-dubatar magoya.bayan Xan takarar shugabacin Kasarnan a jam’iyyar NNPP Injiniya Dokta Rabiu Musa Kwankwaso ne suka taru suka shaidi taron bude ofishinsa na yakin neman zabensa na jihar Kano.

Dokta Rabiu Musa Kwankwaso wanda dubban mutane sukayi rikayi masa shewa na sowar barka da zuwa a yayinda yaje ya ya qaddamarda ofishin na yaqin zabensa dake a unguwar Sharada.
A takaitaccen jawabinsa bayan kaddamarda bude ofishin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi kira ga al’ummar kasarnan  musamman matasa da cewa ranar zabe su tsaya suyi abinda ya dace wajen zabar jam’iyyar NNPP.

Sanata Dokta Rabiu Musa Kwankwaso yaci alwashin kyautata jin dadin al’umma da samawa matasa ayyukanyi da kyautata harkar ilimi a kowane mataki a Nijeriya.

A yayin taron dai Kwankwaso na tareda rakiyar Dan takarar Gwamnan Kano a jam’iyyar NNPP Abba Kabbir Yusuf da Mataimakinsa Kwamared Abdussalam Gwarzo da Sanata Rufa’i Sani Hanga Dan takarar Sanatan Kano ta tsakiya da jigo a jam’iyyar a kasa.Injiniya Buba Galadima da yan takarar majalisun tarayya dana Sanatoci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *