Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta cafke wakilin jaridar Leadership Umar Muhammad Maradun ba tare da wani dalili ba.

An kama Umar Maradun ne a garinsu Maradun da sanyin safiyar ranar Asabar, kuma aka kai shi sashin binciken manyan laifuka na jihar da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Kungiyar ‘yan jarida ta Nijeriya,reshen   jihar Zamfara da wasu mambobin kungiyar  sun je sashen binciken manyan laifuka (CID) na jihar domin neman belinsa amma ‘yan sanda sun ki bayar da belinsa.

Shugabannin kungiyar dai sun ce doka ta tanadi cewa ba a tsare mutun sama da sa’o’i 24 , suna mamakin dalilin da ya sa ba za a bayar da belinsa ba tunda tunda laifin da ake zarginsa ba yana cikin manyan laifuka ba ne.

Da aka tuntubi kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Ayuba N.Elkanah ya ce zai binciki lamarin kuma ya san abin da zai yi.

Elkana ya ce, zan duba lamarin.” Amma bai yi karin bayani ba.

Shugaban NUJ din ya dage da cewa a saki abokin aikinsu, inda ya tabbatar wa ‘yan sanda cewa zai dawo tare da shi ranar Litinin, amma hukumar ‘yan sandan ta ki amincewa da bukatar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *