Daga Abubakar Muhammad Tahir

Yan bindiga dauke da muggan makamai sun hallaka Jami’in shige da fice tare da raunata biyu daga cikin jami’an hukumar.

Cikin wata ganawa da manema labarai da Shugaban Hukumar na Jihar Jigawa Comptroller ACG Ismail Abba yayi da mana labarai a jiya Laraba a Birnin Dutse,ya bayyana cewa lamarin ya faru da misali karfe 11:20 na dare lokacin da yan bindigar suka nufo shige duba kaya hukumar dake yankin Birniwa-Galadi.

Ya kara da cewa ‘Yan bindigar sun zo a mashina guda biyu wanda daya yaga cikin mashin ɗin yana dauke da mutum 3 dayan kuma mutum 2.

Zuwan su ke wuya suka bude wuta kan jami’an hukumar inda a take Daya daga cikin jami’in hukumar mai suna Abdullahi Mohammed (CIA) ya rasa ransa, Abba Musa Kiyawa(DSI) da Zubairu Garba(AII) suka samu munanan raunuka.

Haka kuma ACG Ismail Abba ya kara da cewa sakamakon bata kashi da jami’an nasu, ‘yan bindigar sun jefar da mashi nan nasu da wayar hannu ƙirar Tecno T5 suka shiga jeji.

Mashinan masu Chasis Number MD2A18AXS7MWK81092 da RY157FMINILI2607 ya zuwa yanzu suna hannun jami’an hukumar.

Tuni de aka garzaya da biyun daga cikin wanda suka rasa ransu haka kuma jami’an daya rasu An masa Jana’iza kamar yadda addini Islama ya tanadar.

Nayi n farin ciki da namijin kokarin jami’an hukumar mu wajen yin bata kashi da wadannan maharan har suka jefar da Mashin nansu da wayarsu suka ranta a nakare a cewar Shugaban Hukumar.

Wannan ya kara tabbatar mana jami’an hukumar mu suna aiki tukuru wajen dakile ayyukan taaddanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *