Daga lbrahim Muhammad Kano.

‘Yan siyasa magoya bayan takarar shugabancin kasa na wazirin Adamawa.Tsohon mataimakin shugaban qasa Atiku Abubakar a qarqashin jam’iyyar PDP na jahar sunyi kira ga dan takarar shugaban kasar akan ya tabbatarda Alhaji Ibrahim Al-amin Little a matsayin jagoran yakin neman zabensa.
Yawanci yan jam’iyyar PDP na Kano suna nuna gamsuwarsu da baiwa Ibrahim Little shugabancin kulada takarar Atikun a Kano ne domin gamsuwa da gaskiyarsa da rikon amana kuma zai yi aiki tukuru domin tabbatarda nasara.
Sun kara da bayyana Little da cewa dama shi dan siyasa ne daga tushe wanda yake tareda jama’a kuma kofarsa a bude take ga kowa da yake mu’amala cikin girmamawa da karamci wanda bashi jagorancin yakin Neman zaven na takarar shugabancin kasa na Atiku Abubakar  a Kano zai karawa PDP karsashi da goyon baya.
Wasu na nuna cewa Alhaji Ibrahim wanda daya ne daga wadanda suka nemi tsayawa takarar Gwamna a jahar Kano da cewa mutum ne da zai yi amfani da abinda yake dashi wajen tallata wannan takara dan sunyi kira da budaddiyar murya akan lallai a sanya Ibrahim Al-amin Little a jagorancin yakin zaben neman shugabancin kasa na Atiku a 2023.
Wannan kiraye-kiraye na zuwa ne a daidai lokacinda ake bayyana sunan wani jigo a jam’iyyar da cewa shine daraktan yakin zaben na Atiku a Kano wanda da dama yan jam’iyyar PDP ke kalubalantar hakan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *