Daga Ibrahim Muhammad Kano

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama matasa 83 da zargin aikata fashi da manyan makamai akan al’umma a yayin bukukuwan karamar Sallah.

 

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano S P.Abdullahi Kiyawa ne ya bayyana hakan a wani sako da ya rabawa yan jarida.

 

Ya ce matasan an kama sune a lunguna da sakuna a fadin jihar Kano da yawancin wadanda aka kama sun fito da kayan makamai da yunkurin yiwa mutane fashin waya da jakunkunan mata.

Ya ce wasu kuma an kamasu da sai da miyagun kwayoyi wannan kuna nasara ce duba da yanda ake kuka da bata gari musamman masu fitowa da makamai kala-kala da yunkurin yin kwace su yiwa mutane rauni har da kisa.

Ya ce rundunar yansandan ta samo kayayyaki daga wajen bata garin da suka hada da wayoyi da jakunkunan mata da kwamfutoci da sauran kayayyaki da wasu an baiwa masu shi kuma ana cigaba da bincike.

Wasu daga matasan da aka kama sun amsa laifukansu na cewa sun yi kwace.Rundunar yansandan tace zata gurfanar da wadanda aka kama a kotu da zarar sun gama bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *