Daga Bello Hamza, Abuja

Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana wata sanarwa da jam’iyyar APC reshen Zamfara ta fitar, a matsayin shisshigi don neman suna daga jam’iyyar da ta gaza farfaɗowa daga magagin faɗi zaɓe.

Jam’iyyar APC ta fidda sanarwar ne tana ƙalubalantar gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, bisa zancen da ya yi na cewa tsohon gwamna Bello Mohammed Matawalle ya kwashe tare handame motocin gwamnati da sauran abubuwan amfani a gidan gwamnatin dake Gusau.

Gwamnatin ta Zamfara a wata takardar sanarwar manema labarai wacce mai magana da yawun gwamna, Sulaiman Bala Idris ya fitar yau a Gusau, ta ce sumbatun da APC ke yi, ba komi ba ne face ƙoƙarin bada kariya ga handama da badaƙalar da Matawalle ya aikata. Wanda wannan ke nuna irin halin da jam’iyyar ta APC ke ciki.

Sanarwar ta bayyana cewa: “gwamnatinmu tana nan kan ƙudurinta na ganin ta cika alƙawurran da ta ɗauka lokacin yaƙin neman zaɓe, wanda a ciki har da batun bin diddigin irin ɓarnar da aka aikata a gwamnatance don ƙwatowa jama’a haƙƙinsu.

“Wannan sanarwar ta rashin kan gado da APC ta fitar, sun yi ne da zimmar ɗauke mana hankali daga ayyukan da muka fara don tsamo Zamfara daga halin da take ciki. Lokacinmu yana da tsada, ba za mu tsaya ɓata shi wurin musayar yawu da jam’iyyar da ta kwashe shekaru huɗu kan mulki ba tare da ta yi wa jama’a komi ba, sai dai ma tulin almundahana da waushe asusun jiha.

“Muna da hujja da alƙalumma da suka fallasa irin ta’asar Matawalle. Amma saboda rashin ta-ido shi ne har APC reshen Zamfara ke da bakin magana. Tsohon gwamna Matawalle ya bayar da kwangilar sayo motocin gwamnati kan kuɗi Naira Biliyan 1,149,800,000.00; wanda aka ba kamfanin Hafkhad Properties and Facilities Management Nig. LTD.

“Matawalle ya biya waɗannan maƙudan kuɗaɗe ne domin a sayo motocin gwamnati kamar haka: Toyota Lexus VIP 2021 (me sulke); Toyota Land Cruiser VIP 2021 (mai sulke); Toyota Prado V6 2021; Toyota Prado V4 2021; Peageot 2021; Toyota Hilux 2021; Toyota Land Cruiser 2021 (mai sulke); da kuma Toyota Lexus 2021.

“A ranar 4 ga watan Oktoba 2021, tsohon gwamna ya biya Naira 484, 512, 500.00 ga kamfanin MUSACO domin su kawo motoci uku ƙirar Jeep masu sulke; haka nan an sake ba shi aikin kawo motoci ƙirar Prado Jeep da Land Cruiser guda bakwai akan Naira 459, 995, 000.00; sai kuma aikin kawo motocin Toyota Hilux guda bakwai akan kuɗi Naira 228, 830, 000.00.

“A ranar 19 ga watan Mayun 2021, tsohon gwamna Matawalle ya biya naira miliyan 61, 200, 000.00 ga kamfanin TK Global Services domin a sayo motoci ƙirar Peugeot 406 guda 30. Haka kuma a ranar 15 ga watan Disamba 2021, Matawalle ya ba kamfanin Nadeen Butta aikin sayo mota ƙirar Land Cruiser (mai sulke) kan Naira Miliyan 130, 000, 000.00.

“A ranar 26 ga watan Fabrairu 2022, tsohon gwamna ya ba kamfanin Dapiyau B. Linus aikin sayo motoci biyu ƙirar Land Cruiser Jeep kan kuɗi Naira miliyan 160, 000, 000.00; a ranar 20 ga watan Maris 2022, tsohon gwamnan ya sake biyan MUSACO naira miliyan 120, 000, 000.00 aikin kawo motoci guda uku, waɗanda za a ajiye a ofishin mataimakin gwamna.

“Banda tsabar rashin daraja irin na APC reshen Zamfara, irin wannan taɓargaza, wawura da ɓarna suke ba kariya. Duk motocin da aka zayyano a sama babu wacce take nan, duk su Matawalle sun kwashe su. Wannan abin kunya da me ya yi kama?

“Tuni mun turawa tsohon gwamna Matawalle takardar neman bahasi kan motocin da aka kwashi biliyoyi daga asusun gwamnati aka sayo su, mun ba shi wa’adin kwana biyar.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *