Daga Bello Hamza, Abuja

Ayayin da ake shirin zaben shugabannin majalisa ta 10 ta tarayyar Nijeriya a mako mai zuwa, wata kungiya mai suna ‘North East Youth Organization Forum’ ta yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da ka da ya yi dora dosa a majalisar, ya bari ‘yan majalisar su zabi wanda zai jagorance su.

Wannan kira ya fito ne daga shugaban kungiyar, Alhaji Abdulrahman Buba Kwacam a yayin da yake ganawa da manema labarai a Abuja.

Buba Kwacam y ace sun samu labarin cewa; “wadanda ba sa son ci gaban Nijeriya ba sa son ci gaban kasar nan suna son su kawo mana rudani da tashin hankali da fitina a cikin kasa kuma rashin gaskiya da adalci shi ya haifar da duk wani ta’addanci a Nijeriya. Yakamata kasar Nijeriya mun wuce wannan matsayi a yanzu matsayi ne wanda Yakamata mu dinga aiki da ilimi da hankali da basira”, ya lurantar.

Ya ci gaba da cewa; a zaɓen da yake zuwa yanzu wanda za a yi sati mai zuwa na shugabannin majalisa sun samu labarin cewa za a yi watsi da hukuncin kotu wajen cafke wasu daga cikin wadanda suke neman takarar kujerar shugabancin majalisar Dattawa, da kuma Kakakin majalisar Tarayya; “domin biyan bukatar. Na’am idan an kama su bayan an gama zabe a ce za a sake su. Toh mu fa ba za mu yarda irin wannan abu yan faruwa a kasar nan ba”, inji shi.

Buba Kwacam ya kara da cewa; “abun nan yana shawagi ne kan Mutane guda biyu a kan Akpabio da Abdulaziz Yari. Sannan a yanzu ana kokari a yi watsi da hukuncin kotu a kama Abdulaziz Yari ba bisa ba ka’ida ba bayan an kammala zabe a sake shi. Mu kuma Nijeriya mun san wannan magana, mun zuba ido muna gani. Kuma ba za mu yarda da wannan ba. Wadanda suke shirin wannan abu kar su jefa wannan kasar cikin masifa da bala’i domin ko waye a Nijeriya an zabe shi ne bisa radin al’ummarsa suka zabe shi ba wanda aka tilasta wa a ka zabe wani. Ko shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da a ka zo ana kutin kutin akan ba a son sa ba za a zabe shi ba da a ka je wajen shugaban kasa Muhammadu Buhari me Buhari ya fada? Ya ce kuje ku zabi duk wanda kuke so”, ya labarta.

Shugaban kungiyar ya ce idan har aka kakabawa mutane shugabancin majalisa, a cewarsa shugaba Bola Tinubu zai fuskanci matsalolin da suka hada da; “Tinubu zai gamu da cikas a kan wanda a ka kawo shi ba bisa ka’ida ba. Tun da shi an zabe shi ne zababben shugaban kasa don haka ba dole bane ya yi abin da talakawan kasa suke so. Sai abin da kalilian na al’ummar Nijeriya suke so. Don haka ya bar ‘yan majalisa su je su yi zaben su tsakaninsu da Allah su zabi duk wanda suka ga dama shi ne an yi wa Nijeriya adalci an yi wa gwamnatin Tarayya adalci an yi wa talakawan Nijeriya adalci amma in za a yi dauri dosa ko kuma a je a kama wasu a ajiye. Abin da zai biyo baya har shugaban kasar ba zai ji dadi ba. Don haka shi ne abun da muke kira gare shi”, inji shi.

Ya kara da cewa; “Ya za a yi a ce an daura majalisa wanda ita ce harshen kasa ita ce dukiyar kasa ita ce al’ummar kasa a ce an kakaba mata shugabanni a ce za a samu zaman lafiya ma a kasar wannan abu ne wanda ba zai taba faruwa ba. Kuma wannan majalisar nan mutane ne masu hankali Dattawa ne masu ‘ya’ya masu jikoki wanda suka san gobe suka san jiya suka san yau a kasar nan su ne suke wannan majalisa a ce har suka su yarda a kawo masu shugaban da ba sa so sun cuci al’ummar kasar nan sun cuci kasar nan kuma sun cuci gwamnatin tarayya”, ya ce.

Ya kuma yi kira ga ‘yan majalisar da ka da su zama ‘yan amshin shata, su zama wanda suke so, ka da kuma su yarda da dori dosa. “Duk wani dan majalisar tarayya muna kiran da ya san cewa fa ya cika cikakken mutum ne a ka kawo shi wannan wuri kuma ya san darajar kan sa ya san darajar ‘ya’yan sa a ka kawo shi wannan wuri kar su zamo ‘yan amshin shata sai abin da wasu suke so don a masu. Suna da ‘yancin su kawo ma kasar nan abu mai kyau yadda kasar nan za ta gyaru don haka su guji maganar da wasu za su gaya masu ko su nemi alfarma a zaben masu abun da ba shi ne alheri ga al’ummar kasar nan ba. Ku tafi Majalisa su je su zabi shugabanni wadanda za su taimaki kasar nan mu kuma al’ummar kasar nan muna goyon baya su dari bisa dari. Amma don a kawo wani dori dosa ba za mu yarda ba kuma muna rokon su su ceci kasar nan ciki fitinun da take ciki. Kar su yarda da wannan zaluncin da ake so a yi”, ya ce.

A karshe ya ce yanzu al’ummar Nijeriya sun zuba ido ga gwamnati da jam’iyyar APC domin ganin yadda zaben majalisar za ta gudana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *