Daga Nasiru Adamu

Sakamakon yanayin rashin da’a da gurbacewar al’umma da ake ciki. Karamar hukumar sabon gari ta dauki kudirin fidda wasu dokoki 3 karkashin kulawar hukumar HIZBA, domin kawar da wadannan gurbatatun dabi’un da suke tunkarar al’ummar ta Sabon garin.

 

Sakamakon haka ne majalisar dokokin Karamar hukumar ta Sabon gari ta yi taron gangamin jin ra’ayoyin wakilan al’umma daban daban dangane da wadannan gudurorin.

 

Shugaban Majalisar Hon. Aminu Yusif kuma Kansilan Samaru shi ya jagoranci zaman, yayinda ya karanta kudurorin Majalisar tasu kamar haka

 

Dokokin za su shafi hana yara kanana yawaceyawacen bin Bola da gidajen al’umma don neman kayan Nauyi dake haifar da sace sace ga wasu daga cikin yaran, sai doka ta biyu wadda zata kumshi hana tallace tallacen batsa da wasu masu tallan magungunan gargajiya suke yi akan tituna da kasuwanni, da kuma, doka ta uku da zata shafi kula da wasu gidajen da ake kai Matan aure da kananan yara da ake zinace zinace da su, dake cikin karamar hukumar.

 

Bayan karananto wadannan kudurorin wakilan al’umman sun yi na’am da wadannan kudurce kudurcen,

Saidai sakamakon korafe korafen da wasu wakilan suka gabatar na rashin samun wadataccen lokacin nazartan takardan da hukumar ta mika musu a kurarren lokaci, da bai basu damar iya bada tasu gudun mowar ba na shawarwarin da ake badawa, yasa shugaban taron ya dage wannan zaman zuwa wani lokaci nan gaba kadan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *