Daga Bello Hamza
Ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP kuma tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ya jaddadawa Ɗan takarar gwamnan Jihar Zamfara, Dr. Dauda Lawal cewa zai yi aiki tuƙuru wurin ganin jam’iyyar PDP ta lashe zaɓen 2023 a Jihar da ma ƙasa bakidaya.

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasan ya bayyana haka ne jiya laraba a gidansa dake Abuja, yayin da Dauda Lawal ya jagoranci tawagar ‘ya’yan PDP na Jihar Zamfara tare da wasu jiga-jigan ‘yan siyasa da suka sauka sheƙa daga APC zuwa PDP.

Atiku ya ce, hanya daya ce za a iya bi wurin ceto Zamfara, shi ne ta hanyar korar APC daga mulki.
“Ba za mu samar da nagartacciyar rayuwa ga jama’a ba har sai mun tabbata mun kori APC, wanda kuma hakan na buƙatan hadin kai.
“Babban abin da mutanen Zamfara ke buƙata a yanzu shi ne zaman lafiya. A samar da tsaro a gonaki, a samar da ayyukan yi. Idan aka yi haka, za a samu inganci a komi na rayuwa” Inji shi

Tun farko a jawabinsa, dan takarar gwamna na PDP a Zamfara, Dr. Dauda Lawal ya bayyana dalilin wannan ziyara a matsayin gaisuwa tare da gabatar da jiga-jigan ‘yan siyasar da suka sauya sheƙa daga APC zuwa PDP. Haka nan kuma don taya murna ga Atiku bisa nasarar da ya samu a zaben fidda gwanin PDP wanda aka yi kwanakin baya.

Lawal ya ce, ‘yan Nijeriya sun gaji da APC, a shirye suke da su zabi PDP a matakin jihohi da ma tarayya. “Samun waɗannan manyan ‘yan siyasa su sauya sheka daga APC zuwa garemu, ba ƙaramar nasara ba ce ga PDP”. Inji shi.

Daga cikin jiga-jigan da suka sauya shekan daga APC zuwa PDP akwai Alhaji Salihu Mai Buhu Gummi, Alhaji Sahabi Liman Kaura, Alhaji Illili Bakura, Engr. Garba Ahmad Yandi, Hon. Ikra Bilbis, Dr. Na’Allah Isa Mayana, Hon. Mukhtar Lugga da sauransu.

Kafin kammala ziyarar, Dauda Lawal ya gabatarwa da Atiku da kyautar rigar saka a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan da Zamfara ta shahara da su a baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *