Daga Ibrahim Muhammad Kano

Sanatan kano ta tsakiya Rufa’i Sani Hanga ya ce alkawarurru ka da suka yi lokacin yakin neman zabe da yardar Allan suna nan tafe za’a cika su ya ayyana haka ne a lokacin walimar daya gudanar na ga magoya bayansa.

Ya ce walimar ta biyo bayan rantsar dasu da akayi ne a Abuja wanda mutane basu sami damar zuwa ba sakamakon yanayi na ka’idoji da aka sanya,dan haka ya shirya walimar dan a yiwa jama’a godiya da jaddada alkawura da suka yi a yakin neman zabe, da fahimtar dasu cewa da yardar Allan suna tafe za’a waiwayi jama’a.

Ya ce za su yi iya kokarinsu daidai gwargwado na waiwayar jama’a da tallafa musu,za su yi tallafi kala-kala na koyawa mutane sana’oi da basu jari da na lafiya da samawa mutane aiki daidai gwargwado da samawa yara tallafin karatu.

Ya ce akwai tallafi na koyawa mutane ayyuka a dauki yan mata da aka koyawa aikin gyaran gashi da wadanda aka yiwa tallafin rashin lafiya yanzu ma ana duba marasa lafiya a Dala ana basu magani kyauta.Nan gaba duk za’a je kananan hukumomi na kano ta tsakiya a basu tallafin magani.Akwai tsari ta hannun shugabanni da za’a rika tallafawa mutane da yin ayyuka da suke da bukata.

Sanata Hanga ya ce aiki Uku ne a gabansu na yin doka da duba ayyuka dan tabbatar kudade da aka ba ma’aikatu suna kashe su yanda yakamata da aiki na waiwayar mutane dan ayi musu ayyuka da yakamata a taimaka musu daidai gwargwado.

Sanatan ya ja hankalin mutane su sani sanata ba gwamna bane,ba shugaban karamar hukuma ba ne,basuda kudin kaso na kasa amma za su shiga su fita dan nemo abin taimakawa al’umma, abinda suke bukata a wajen jama’a shine a bisu da addu’a Allah ya basu yin abin alheri wanda ya fito karfinsu yasa sufi karfinsa dan waiwayar jama’a da taimaka musu.

Shima a jawabinsa jigo a jam’iyyar APC a jihar Kano. Ambasada Ahmadu Haruna Zago ya yi kira ga al’umma su sa tawwakali a zukata su yi abinda yakamata saura su barwa Allah.

Dan zago ya ja hankalin mutane da cewa Kar su dauka sun yi wahala su ba’ayi musu ba.Allah ya rubuta arzikinsu ta inda ba su su yi tsammani ba.

Ya yi kira ga al’umma musamman gwamnatin Kano da ta zo da yardar mutane da amincewarsu, ba ta da gwamnatin tarayya bare ta jiha ko karamar hukuma ko yan majalisu, haka Allah ya kawota.Dan haka al’umma su bata hadin-kai su taimaka mata ta addu’oi da shawarwari a kuma kaucewa yin abubuwa da basu kamata ba, idan aka yi haka a irin kudurin gwamnatin a hangensa, jama’a za suce sam barka.

Shima a jawabinsa shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano. Hon.Haruna Doguwa da ya wakilci gwamnan Kano ya yi fatan alkhairi ga sanata Hanga.

Da yake zantawa da yan jarida jagoran yakin zaben Sanata Hanga kuma shugaba na ofishinsa Ahmad Tijhani Usman ya ce taron na dan aike ne, da aka aika, ya je aka rantsar dashi ya zo ya yi godiya.

Ya ce ya zo ne ya shaida musu an rantsar dashi zai koma ya kama aiki na wakilci ya kuma jaddada musu komai sai da shawararsu zai yi kuma ba zai aikin gaban kansa ba sai na bukatar al’umma.

Ya ce ya godewa Allah da ya basu nasarar samun wakili da zai yi jagoranci yanda yakamata domin Kano ta tsakiya itace rabin Kano mafiya rinjayen mutanen jihar a Kano ta tsakiya suke. Ba karamar nasara ba ce samun wakili da ya koshi da hankalin da ilimi da mutuntaka da kyakkyawan nasaba da zai abinda ya dace ga wadanda yake wakilta.

Shehu Tijjani Usman ya ce dama ba sabo ne ba,ya taba zama sanata Yanzu. zuwa zai je da kwarewa da manufofi da za su kawowa Kano cigaba ta yin kudurce-kudurce.

Taron ya sami halartar mutane da suka hada da yan siyasa da malamai da sauran mutane da dama.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *