Daga Ibrahim Muhammad Kano
Sabon kwamishinan ayyuka na musamman da Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya Nada.Hon.Kabir Muhammad Tarauni yace zasu bada gudummuwa sosai dan ganin an sami nasarar lashe zaben Dan takararsu na Gwamnan jahar Kano karkashin jam’iyyar APC mataimakin Gwamnan Kano.Dokta Nasiru Yusuf Gawuna da mataimakunsa Hon.Murtala Sule Garo a save mai zuwa.
Yace su da suka fito daga gidan siyasar Salihu Sagir Takai zasu bada gudummuwa gaggaruma wajen ganin jam’iyyar APC ta kai ga nasara run daga sama har kasa.
Hon.Kabir Muhammad Tarauni ya yiwa Allah godiya bisa wannan dama da aka bashi ya godewa Gwamnan Kano Dokta Ganduje bisa nada shi kwamishina.
Yace a Tarauni jam’iyyar APC ake dodar kuma a halin yanzu jihar Kano ta dauki saiti babu wani dan takara fiyeda Nasiru Yusuf Gawuna dan mutumne na kirki Dattijon arziki ga kuma mataimskinsa Murtala Sule Garo Kwamandan kwamandoji.
Hon.Kabir Muhammad Tarauni yaceGwamnan Kano Ganduje ya yiwa jihar Kano ayyuka da dama da a tarihin Kano ba za’a taba mantawa dashi be dan haka yanzu a Kano ba wata jam’iyya mai motsi sai APC me kayan gwari ta lalace PDP kuma ba’a san ma waye dan takararta ba a jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *