Daga Bello Hamza, Abuja

A halin yanzu zabbaben Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya zabi mutum 60 da za su kasance a cikn kwamitin karbar mulki daga gwamnati mai barin gado.

A ranar Laraba ne sanarwar haka ta fito daga ofishin watsa labaran sabon gwamnan inda babban jami’I a ofishin, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa sanarwar hannu, ya kuma ce, ana sa ran kwamitin zai tattauna ne da gwamnati mai barin gado karkashin jagorancin Gwamnan Bello Matawalle a kan shirye-shiryen karbar mulki a ranar 29 ga watan Mayu 2023.

Tsohon shugaban rundunar ‘yansandan Nijeriya, MD Abubakar CFR, ne zai shugabanci kwamitin yayin da Dakta Hamza Mohammed zai zama sakataren kwamitin.

Cikin mambobin kwamitin kuma akwai tsohon shugaban ma’aikatan Jihar Zamfara, Mujitaba Isah Gusau; Kanal Bala Mande (mai ritaya); Farfesa Abubakar Aliyu Liman; Barista Nura Ibrahim Zarumi; Barista Bello Galadi, da sauran su.

An tattaro ‘yan kwamitin ne daga kwararun ma’aikatan gwamnati masu ci da kuma wadanda suka yi ritaya daga bangarori na rayuwa al’umma da dama don kasancewa a kwamitin.

Babban aikin kwamitin in ji sanarwar, shi ne samar da yanayi tare da tsara tattaunwa tare da fito da tsarin karbar mulki daga gwamnati mai barin gado zuwa gwamnati mai kamawa ba tare da wata matsala ba.

Haka kuma kwamitin zai duba ayyukan ma’aikatu da hukumomin gwamnati tare da lura da yadda suka kashe kudaden gwamnati da sauran harkoknsu.

Za a sanar da ranar kaddamar da kwamitin a nan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *