Daga Ibrahim Muhammad Kano
‘Yan Darikar Tijjaniyya Faidha ba za su zabi duk wani shugaba a kasarnan ko Dan takararka Gwamna ba said Wanda zai mutunta darikarsu.Malamin Jami’an nan kuma dan siyasa Wanda kuma shine Kwamishinan al’amuran addini a Gwamnatin jihar Kano.Dokta Muhammad Tahar da akafai sani da Baba Impossible ne ya bayyana haka da yake jawabi a wani taron kungiyar Mata na Inuwar Tijjaniyya da Faidha suka gudanar a ranar Asabar a dakin taro na masallacin Shehu Ahmad Tijjani sake kofar Mata.
Ya ja hankalin matan yan Tijjaniyya da Faidha da cewa”My zabi namu a kowace jjam’iyya yake,in an sami wani Dan majalisa a jam’,iyya mai Doki kuma namunne to a zabe shi,in kuma akaga wani yana Gwamna a me Agwagwa to in acan namu ne to a zabe shi”.
Ya yi nuni da cewa yan Tijjaniyya da Faidha sun sha yin zabe anyi Gwamnati a sama bata taimakesu ba,an yi a kasa bata taimakesu baDan haka wajibi su tsaya a wannan karon su duba duk Wanda zasu zaba ya zama nasu ne a kowane mataki na zabe kuma a kowace jam’iyya.
Itama da take  zantawa da yan jarida ciki harda wakilin jaridar idon mikiya shugabar Inuwar matan Tijjaniyya da Faidha. Sayyida Fatima Muhammad Tahar tace taron karo na biyar ne da take yinsa dan wayar da kan mata kan darikar Tijjaniyya da abubuwanda yake cikinta dan tantance abinda yake daidai da Wanda na daidai ba dan a kau dashi.Iron wadannan taruka zai kara musu ilimi.
Sayyida tace kira da kwamishinan al’amran addini ya yi a taron na cewa su zabi duk dan takara da ya kasance dan Tijjaniyya ne da Faidha da cewa kira ne mai kyau kuma da yardar Allah sun amsa domin dama su yakamata ace sune suke da yawanda zasu iya bada shugabanci.”In Allah ya taimaka ka fito ka zabi Wanda zai kara mutuncin abinda ka keyi said muce kwalliya zata biya kudin sabulu”cewarta.
A yayin taron daya sami halartar dinbim Mata daga ciki da wajen jihar Kano a gabatarda jawabai da  wakokin Gayon Manzon Allah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *