Daga Umar Faruk Brinin Kebbi

Babbar Kotun Gwamnatin Tarayya da ke zamanta a Brinin Kebbi, a karkashin jagorancin Mai Shari’a Babagana Ashigar ta fara sauraren karar da Shehu Muhammad Bello Koko ya shigar a gaban kotun.

Shehu Muhammad Bello Koko, ya shigar da karar ne  kan kalubalantar Shehu Muhammad Koko Dan majalisa mai wakiltar mazabun kananan hukumomin Koko da Maiyama a majalisar dokokin na tarayya, Hukumar zabe mai kanta da kuma Jam’iyyar APC kan kotun  ta tabbatar dashi a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani  na kujerar dan takarar  majalisar Koko-Maiyama a majalisar dokokin tarayya da aka gudanar a ranar 27 ga watan Mayu na shekara ta 2022 a karamar Hukumar Maiyama, bisa ga hujojin da zaya gabatar ta hannun lauyansa Barista Hussaini Zakariya SAN.

Yayin zaman kotun na yau, lauyan mai kara Barista Hussaini Zakariya SAN ya bayyana wa kotun cewa” bisa ga umurnin kotu dukkan takardun kara an aikewa dukkan wadanda ake Kara kuma yanzu hakan Lauyoyin wadanda ake Kara na a gaban kotu, inji lauyan mai kara Barista Hussaini Zakariya”. Haka zalika ya kara da cewa” duk da yake kwanakin da doka ta basu na sanya na su takardu wa’adin bai kare ba don sai ranar 3 ga watan Yuli na shekara ta 2022 ne zai kare, inji shi”.

A martanin  Lauyoyin da ke tsayawa wadanda ake Kara sun   tabbatar wa kotun cewa” sun karbi dukkan takardun na shigar da karar da lauyan mai kara ya sanya a gaban kotun, inji su”. Bisa ga hakan suka nemi kotun ta kara musu dama don kammala shigar dukkan takardunsu  a gaban kotun don har yanzu suna da sauran lokaci da doka ta basu.

Lauyan da ke gabatar da kara, Barista Hussaini Zakariya SAN ya nemi kotun da ta dage sauraren karar har zuwa ranar 11 ga watan Yuli na shekara ta 2022 don dawowa a cikin gaba da sauran karar, wanda hakan zai baiwa wadanda ake kara   damar kammala shigar da dukkan takardun su a gaban kotun.

Bugu da kari, Lauyoyin wadanda ake kara sun amince da dage sauraren karar bisa ga bukatar da lauyan mai kara Barista Hussaini Zakariya SAN ya nemi a gaban kotun.

A nata bangare, kotun ta sanar da dage sauraren karar har zuwa ranar 11 ga watan Yuli na shekara 2022 don dawowa a cikin gaba da sauraren karar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *