Daga Shu’aibu ibrahim Gusau

Shugaban Kwamitin yada labarai na yakin ne man zaben Gwamna Bello Matawalle, Alhaji Ibrahim Danmaliki ya jaddada kudurin jam’iyar su na cewa ba za ta bari ‘yan bangar siyasa suyi amfani da muggan makamai a yakin neman zabe ba.

Alhaji Ibrahim Danmaliki ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan shirye-shiryen yakin neman za be Wanda zai gudana a Kaura Namoda ta jihar Zamfara .

Ya ci gaba da cewa an sanar da jami’an tsaro masu yaki da ‘yan daba su kama duk wanda aka samu da makami tare da gurfanar da su a gaban kuliya da kuma duba ayyukan ‘yan daba a lokacin yakin neman zaben da kuma bayan yakin neman zaben domin APC ba za ta amince da irin wannan dabi’a ba.

Ya kuma ce an kafa kwamitoci daban-daban da za su gudanar da dukkan harkokin yakin neman zabe domin ganin komai ya tafi lami lafiya kamar yadda aka tsara, ya ce za a gudanar da yakin neman zaben ne a gundumomin Sanatocin jihar guda uku kafin a koma dukkanin kananan hukumomin jihar.

Ya yi kira ga ‘yan jarida da su ba da goyon baya tare da tabbatar da isassun rahotanni na gaskiya ta hanyar yakin neman zabe kamar yadda za a gudanar da su.

Danmaliki ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da marawa APC baya a matsayinta na jam’iyya mai mulki a jihar da ma kasa baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *