Daga Ibrahim Muhammad.Kano

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa matar shugaban DSS na kasa Bichi ta yi barazanar hana shi zama gwamnan jihar Kano a zaben 2023.

Ya bayyana haka ne a ranar a lokacin da yake tattaunawa da malaman Addinin Musulunci da suka ziyarce shi a gidan gwamnati.

A wani lokaci a baya kafin zabe zaben, an yi ta cece-kuce a kafafen sada zumunta kan rikicin da ya barke tsakanin magoya bayan Abba Kabir Yusuf da uwargidan shugaban DSS a filin jirgin saman Malam Aminu Kano.

Gwamnan, koka kan yadda wasu malaman Addinin Musulunci suka je gidajen rediyo suna zarginsa ba tare da sanin hakikanin abin da ya faru tsakaninsa da Matar Bichi ba.

Yace bayan jami’an DSS sun ci mutuncin mutanensu, sai ya kai mata korafi, sai ta fara zaginsa, ta ce ta rantse ba za su taba bari ya zama gwamnan jihar Kano ba.

Gwamnan ya kuma yi zargin cewa uwargidan shugaban ta DSS din, ta hana shi shiga jirgin kasuwanci bayan da ya biya kudin tikitinsa, inda ya kara da cewa wasu malaman Kano ma sun yi ta sukarsa duk da cewa shi aka cutar ba tare da jin nasa bangaren ba.

Don haka Abba Kabir Yusuf ya shaida wa malaman da suka halarci taron cewa zai mutunta dukkan malaman Addini a jihar, amma ya yi gargadin cewa ba zai lamunci masu sukar gwamnatinsa ba a cikinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *