Daga Shuaibu Ibrahim Gusau

Babbar kotun jihar Zamfara mai lamba 11 da ke zamanta a Gusau ta dage ci gaba da shari’ar har zuwa ranar 24 ga watan Oktoban 2022 inda ake zargin gwamnatin jihar zamfara ta sayar da taraktocin da kotu ta kama yayin da ake ci gaba da shari’ar.

Alkalin kotun, Mai shari’a Bello Shinkafi ya ce ya dage ci gaba da shari’ar ne biyo bayan rashin halartar lauyoyin masu kara a kotu.

Mai shari’a Shinkafi ya bayyana cewa, kwanaki biyu da suka gabata lauyoyin masu kare wadanda ake kara, ta hannun shugabansu, Mohammed Sadiq Suleiman, ya rubuta wa kotun cewa a dage shari’ar, sakamakon wani zama da suke da shi a babban kotu dake Sokoto.

Tun da farko dai, lauyan wanda ya shigar da kara, John Shaka, ya bayyana cewa bukatar da ta yi na neman a dage shari’ar ba ta da wani hakki, inda ya bukaci alkali da ya yi watsi da bukatar.

Idan ba’a manta ba kotu ta bukaci kwamishinan aikin Gona Daya bayyana a gabatanta ranar 14 ga watan Satumba, sai dai hakan Kuma bai samu ba sai a wannan rana ta 28 ga watan satumba.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *